May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnatin jihar Zamfara za ta kashe sama da Naira biliyan shida domin gina tituna a karamar hukumar Maradun

1 min read
Gwamnatin jihar Zamfara za ta kashe sama da Naira biliyan shida domin gina tituna a karamar hukumar Maradun

Hanyoyin da za a gina su ne titin Maradun – Magami- Faru da Maradun – Makera, domin saukaka zirga-zirga a yankin.

Gwamnan jihar, Dauda Lawal ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ziyarci karamar hukumar kwanan baya, inda ya kaddamar da rabon takin zamani da sauran kayayyakin noma ga manoman yankin da ke karkashin Fadama |||.

A yayin kaddamarwar, gwamna Dauda wanda ya tabbatar wa manoman yankin kudurin gwamnatinsa na tallafa wa fannin noma domin bunkasar noma, ya kuma bukaci wadanda suka amfana da su yi amfani da wannan damar wajen kara yawan amfanin gona da kuma bayar da tasu gudunmawar wajen habaka fannin noma.

Da yake jawabi tun da farko, shugaban karamar hukumar Alhaji Yahaya Giwa Maradun ya nuna jin dadinsa da na al’ummar yankin ga gwamnan kan yadda ya magance matsalar ruwan sha da suka shafe shekaru da dama suna fama da su, cikin watanni shida da mulkinsa a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *