May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Jami’an tsaro a Kano sun kama wata Mata da ke zargin tayi Garkuwa da kanta a hotel

2 min read

Hukumomi a jahar Kano, sun tabbatar da Kama wata matar aure mai suna Sa’adatu Muktar mai shekaru 21 a duniya yar asalin jahar Kaduna , wadda ta ke aure a jahar Katsina, bisa zargin yin garkuwa da kanta a wani Hotel dake jahar Kano.

Jaridar idongari.ng, ta ruwaito cewa, Sa’adatu Muktar, ta baro gidan mijin ta a unguwar Abbatuwa cikin garin Katsina, kwanaki goma da suka gabata, wadda ta yada zango a Unguwar Tishama Kano.

Wadda ake zargin ta yi kwanaki 7 kachal a gidan Wata kawarta mai suna Salma da Suka hadu a jahar Katsina, daga bisani kuma ta koma Unguwar Danbare dake kan babban titin zuwa Gwarzo road a Kano.

Bayana haka matar auren ta koma wani Hotel, a unguwar Sabon Gari Kano, inda ake zargin ta hada Kai wasu mutane mazauna jahar Katsina, har ta kira mijin ta mai suna Abubakar, inda mutanen suka shaida masa cewar, sun yi garkuwa da ita , kuma sai an biya kudin fansa naira miliyan talatin sannan za Su sake ta.

Sai dai Mijin na ta, yaki tura ko sisin kobo daga cikin kudin fansar da aka nema a wajensa, inda ya Fara bibiyar wayar ta har ya gano cewar tana jahar Kano.

Da ya ke yi wa jaridar idongari.ng, karin haske mukaddashin babban kwamandan hukumar hisbah na jahar Kano, Dr. Mujahid Aminuddin Abubakar, ya ce, mijin nata ya zo Kano, kuma ya shigar korafi a hukumar Hisbah , wadanda suka samu nasarar kamo ta a yankin Bama Road dake Unguwar Sabon Gari Kano.

Dr. Mujahedeen Aminuddin, ya kara da cewa, wannan abu ne mara dadin ji, inda matar auren ta yi garkuwa da kanta , bayan ta yi karyar cewa za ta je gida jahar Katsina, amma ta taho Kano.

” Wannan abun haushi ne, wai sai an biya miliyan Talatin , to ka ga yakamata mu dinga Jan matan mu da yayan mu a jiki , don rashin zama da su a tattauna shi ne yake kawo haka” Dr. Mujahedeen “.

Hukumar hisbar ta ce , mijin matar ya shaida mu Su, cewar maganar ta na wajen jami’an Yan sandan jahar Kaduna, shi yasa suka dankata a hannunsa don daukar mataki na gaba.

Suma hukumomin tsaro a Kano da kuma jahar Katsina, an shigar da batun yin garkuwa da ita , a gaban su, kuma tuni Suka baza komar kamo wadanda ake zargin, inda daga baya hukumar hisbar ta kamo ta, a wajen da ake zargin ana aikata masha’a

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *