May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Katsina united ta doke Kano pillars a Wasan mako na 22

1 min read

Kungiyar kwallon kafa ta katsina united ta doke Kano pillars a cigaba da Gasar Premier ta Kasa mako na 22.

Tun da fari dai Katsina ce ta fara jefa kwallo a ragar pillars tun a muntuna 33 da fara a wasa.

Bayan dawo wa daga hutun rabin lokaci ne pillars ta farke kwallon ta ta hannun Ibrahim MUstapha.

Daga bisani ne dai katsina ta Kuma Kara kwallo biyu a ragar pillars.

A Ranar asabar Pillars zata fafata da Abia Warriors a Filin wasa na Sani Abacha dake kofar Mata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *