May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Dalilan da suka sa na dawo Kujerata – Daurawa

3 min read

Shugaban hukumar Hizba na jihar Kano, Malam Aminu Ibrahim Daurawa, ya sanar da cewa ayyukan hukumar za su ci gaba da gudana kamar yadda aka fara na gangamin kauda badala da tsarkake jihar daga bata-gari.

Malam Daurawa ya yi wannan bayani ne jim kadan bayan sulhu tsakaninsa da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf,.

Sheikh Daurawa ya sanar da yin murabus ne a ranar Juma’a bayan kalaman da gwamna Kabir Yusuf na kalubalantar yadda hukumar Hizba ke gudanar da ayyukanta.

Amma a hirarsa da BBC bayan janye murabus ɗinsa, Daurawa ya ce shaidan ne ya shiga tsakani.

“An kawar da shaidan a tsakani an kuma fahimci juna kan manufar ayyukan hukumar da gwamnan na jihar Kano, inda ya ce wannan sabani tamkar taki ya karawa hukumar,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa gwamnati za ta ba su kudaden tafiyar da ayyukan ci gaba da gyaran tarbiyya a jihar.

”Abubuwan da aka fara su za a ci gaba da yi na tsaftace Kano daga badala, da gyaran tarbiyya da hukumar Hizba ta dauko yi. Maigirma gwamna ya ce zai samarwa Hizba kayan aiki da ba ta goyon baya a kan dukkan ayyukan alhairin da ake yi.”

Shehin malamin ya ce gwamnati ba ta karbi takardar murabus dinsa ba, a yanzu kuma sun fahimci juna.

“Gwamna ya roke ni da na ci gaba da zuwa ofis, ya yi alkawarin ba mu hadin kai dari bisa dari, kuma na dawo bakin aikin shugabancin hukumar Hizba in sha Allahu,” in ji Daurawa.

An ƙara zaburar da Hisba’
Wasu dai na ganin abubuwan da suka faru a baya-bayan nan za su kawo cikas ga ayyukan hukumar Hizba, kuma a matsayin Malam Daurawa na kwamandanta tamkar an sanya masa takunkumi ne.

Amma Daurawa ya musanta hakan, inda ya ce an ma karfafa hukumar ne, don haka ne ma suka fito da wani sabon tsari na kara tsaftace ayyukansu.

‘Malamin ya ce hukumarsa ta ba ‘yandaudu da karuwai da duk masu aikata baɗala wa’adin mako biyu, wanda yake son tuba ya zo ya tuba.

“Mun samar da wani fom mai suna na tuba da mutum zai cike. Za a koya ma sana’a da jari, idan ba dan jihar Kano ba ne za a mayar da shi garinsu, wanda kuma bai tuba ba y na ganin zai ci gaba da karya doka, to gara ya tattara kayansa ya bar Kano domin Kano ba matattarar badala ba ce.”

Daya daga cikin maganganun da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi shi ne yadda ma’aikatan Hizbah ke gudanar da samamen kama masu aikata laifi da ya ce hakan bai dace ba ana dibarsu kamar awaki da rarakarsu da gora.

Kwamandan Hizba ya ce za ta ci gaba da inganta ayyukanta, ta hanyar daukar matakan bai wa ma’aikatansu horo, inda ya ce ma’aikatun gwamnati ana samun kurakurai tare da ba da misali da kuskuren rundunar sojin Najeriya ta hanyar jefa bam kan masu mauludi a garin Tudun Biri na jihar Kaduna da ya haddasa mutuwar mutane da dama.

‘Za mu kara inganta aikin ta fannin ilimi da kwarewa, za mu samar da sashen shari’a da na fasahar zamani da za a dinga tantance ayyuka da bibiyarsu. Kuma muna kokarin kafa makaranta mai suna Hizba Training School da za a dinga karatu na matakin NCE da Difloma, har da digiri a kan aikin Hizba,” in ji Sheikh Daurawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *