May 20, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnatin Nigeria ta koka game cigaba da tabarbarewar bangaren Wutar Lantarki

1 min read

Ministan ma’aikatar samar da hasken wutar lantarki a Najeriya, Bayo Adelabu, ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya nuna ɓacin ransa kan raguwar wutar lantarki da ake samu duk da irin kokari da ake yi a ɓangaren.

Ya ce ba za su lamunci rashin samar da wuta ba daga kamfanonin da alhakin haka ya rataya a wuyansu, kuma za a ɗauki mataki mai tsanani a kansu, ciki har da soke lasisi.

Bayo ya buƙaci jama’a da su ƙara hakuri yayin da ake aiki tukuru wajen magance waɗannan matsaloli da kuma samarwa ƴan Najeriya wutar lantarki yadda ya kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *