May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnatin Kano ta sanar da kulle gidajen Gala dake Fadin Jihar baki daya

1 min read

A shirye-shiryen ta na shigowar watan Azumin Ramadana, Hukumar tace Fina-finai da Dab’i ta jahar Kano ta bada umarnin kulle dukkannin gidajen Galar dake fadin jahar Kano.

Wannan na zuwa ne biyo bayan wata ganawa da Shugaban Hukumar yayi da jagororin yan Kungiyar ta masu gidajen galar reshen jahar Kano a ofishin sa.

A cewar shugaban Hukumar Abba El-mustapha, dokar zata fara aiki ne tun daga yau lahadi har zuwa 1 ga watan shawwal wato ranar bikin karamar sallah.

Abba El-mustapha ya gargadi masu gidajen wasannin na gala da su guji Karya doka domin duk wanda Hukumar ta samu da laifin karya wannan dokar to hakika zata dauki tsastsauran mataki a kansa wanda ka iya sawa ya rasa lasisin sa na din-din-din.

El-mustapha ya kuma godewa jagorori tare da yan Kungiyar ta masu gidajen gala hadi da al’ummar jahar Kano dangane da hadin kan da suke bawa Hukumar a kowanne lokaci.

A karshe ya Kara tunatar da dukkannin al’umma cewa kofar sa’ a bude take domin bashi shawara ko sanar da Hukumar duk wani al’amari da zai taimake ta domin samun nasarar aiyukan data saka a gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *