May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Tinubu ya umarci Kwastam ta mayar da kayan abincin da ta kwace wa mutane

1 min read

Babban Kwanturan Hukumar Kwastam ta Najeriya, Bashir Adewale Adeniyi ya ce shugaban ƙasar Bola Tinubu ya umarci hukumar ta mayar da duka abinci dangin tsaba da ta ƙwace daga wajen mutane domin sayar da su a kasuwanni.

Cikin wata sanarwa da hukumar Kwastam ɗin ta fitar a shafinta na X, ta ce mista Adeniyi ya bayyana hakan ne lokacin wata ziyara da ya kai kan iyakar Kwangwalam da ke ƙaramar hukumar Maiadua a jihar Katsina inda ya gana da masu ruwa da tsaki.

Shugaban Kwastam ɗin ya ce umarnin shugaba Tinubun wata alama ce da ke nuna burin shugaban ƙasar na tabbatar da al’ummar ƙasar sun wadata da abinci ta yadda farashinsa zai sauka a kasuwannin ƙasar.

Ya ƙara da cewa sharaɗin mayar da kayan abincin hannun mutanen da aka ƙwace musun, shi ne za su sayar da shi a kasuwannin Najeriya.

Mista Adeniyi ya kuma ce dole ne a samu dangantakar alaƙa tsakanin jami’an tsaro da ci gaban tattalin arziki, yana mai cewa idan babu zaman lafiya da tsaro kasuwanci ba zai inganta ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *