May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Tuni sarkin Musulunci ya Sanar da ganin watan azumin Ramadan a Najeriya

1 min read

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III ya sanar da ganin watan azumin Ramadana a Najeriya.

Hakan na nufin gobe Litinin za ta kasance 1 ga watan Ramadan, wato ranar da al’ummar Musulmi a duka sassan ƙasar za su tashi da azumin wannan shekara.

Ƙasashe da dama sun sanar da ganin watan na azumi a yau, ciki har da Saudiyya.

Ya yi kira da a yi wa ƙasa addu’a, musamman a daidai wannan lokaci da ake fama da tsadar rayuwa da kuma matsalolin tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *