May 20, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Majalisar Dattawan Nigeria ta musanta labarin da ke cewa Al’ummar Niger Delta ne suka kashe Sojoji a yakin

1 min read

Shugaban Majalisar Dattawan Nigeria Sanata Godswil akpabio, yace ba Al’ummar Yankin Niger Delta bane suka Hallaka Sojojin Nigeria 16 ba

Sanata Akpabio Yace Wadanda suka Kashe Sojojin Sun zo ne daga Kasashen Ketare Bisa Daukar Nauyinsu da akayi acewarsa

Ya Kara da acewar al’ummar Yankinsa Masu San Zaman Lafiya ne Dan haka Yana da Yakinin Cewa Ba Al’ummar yankin bane suka aikata Wannan Danyen aiki

Ya bayyana hakan yayin Zaman Majalisar Dattawan Nigeria na jiya Bayan da Majalisar ta Kafa Wani Kwamiti da Zai Gudanar da bincike akan Yadda aka Hallaka Sojojin Nigeria 16 a Jihar Delta

Sai dai Kuma Tuni Kungiyoyin fararen Hula suka Fara Mayar Da Martani ga Shugaban Majalisar Dattawan, inda suka Bukaci da Ya fito Fili ya Bayar da bayanan wadanda suka aikata Wannan Danyen aiki Tunda Yana da Masaniya

Auwal Musa Rafsanjani da shugaban Kungiyar CISLAC da Sauran Kungiyoyin Fararen Hula, Sunyi Allah Wadai Da Kalamam Shugaban Majalisar Dattawan

Suna Mai Cewa Yakamata Yan Siyasa Su Rika taka tsan tsan akan Duk wasu Kalamai da zasuyi akan Wani batu musamman da ya shafi Tsaro

Sai dai Sanata Goodwill akoabio ya Bukaci Addu’oi Domin Gano Wadanda Suka aikata Wannan Kisan Gilla, yayinda ya jaddda Cewa Al’ummar Yankinsa Masu San Zaman Lafiya ne

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *