May 20, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Yadda sojin Najeriya suka kashe ƴanbindiga da lalata maɓoyarsu

1 min read

Sojoji a Najeriya sun kashe wani ƙasurgumin ɗanbindiga wanda ke bayyana kansa a matsayin ɗansanda a Sokoto domin aikata miyagun laifuka.

Ɗanbindigar da aka kashe ranar Laraba yana ɗaukan mutane aiki domin yaudarar su da kuma yin garkuwa da mutanen da ba su ji ba su gani ba.

Wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na rundunar sojin ƙasa, manjo janar Onyema Nwachukwu ta ce an kai samamen ne bayan samun wasu bayanan sirri inda aka kashe mutumin da ake zargi sakamakon musayar wuta da sojoji.

Sojojin sun kuma gano tare da lalata wani gida da mayan ƴanbindigar ke amfani da shi a matsayin sansanin ajiyar magunguna da kuma kula da ƴanbindigar da suka ji rauni.

A wani harin kuma a jihar Taraba, sojoji sun kashe wani ɗanbindiga a ƙauyen Kutoko da ke ƙaramar hukumar Takum inda aka gano bindiga ƙirar AK-47 da alburusai masu tarin yawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *