May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Al’umma da dama na gudun hijira a Zamfara

2 min read

A Najeriya, ‘yan bindiga
na kara matsa kaimi a har-haren da suke kai wa wasu garuruwan Jangebe da Magazu na jihar Zamfara, inda suke sace mutane don neman kudin fansa, bayan sun aikata kisan gilla da barnata dukiyoyin jama’a.

Matsalar hare-haren ‘yan bindiga da ta addabi al’ummar garin Jangebe da wasu kauyukansa akalla biyar, a yankin karamar hukumar Talatar Mafara ta jihar Zamfara, ta kara kwabewa.

A cewar wani mutumin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce tun daga ranar talata har zuwa laraba, kauyukan Jangebe biyar zuwa shida suna cikin iftila’in kashe-kashe.

Mazaunin na Jangebe ya shaida wa BBC cewa a baya an samu saukin lamarin, sai dai kwanan nan abin ya dawo sabo a yankin Talatar Mafara ta Kudu, kuma yawacin mutanen kauyukan yankin, “Muna rokon gwamnatin tarayya da ta jiha su kawo mana dauki.”

A garin Magazu na yankin karamar hukumar Tsafe ma, hare-haren ‘yan bindigan suna kara munana, kamar yadda wani mutumin garin da ba ya so a fadi sunansa ya bayyana wa BBC.

“A baya an samu saukin lamarin sosai, sai dai yanzu abin ya dawo fiye da yadda ake tsammani, ko ranar Laraba sun shiga garin Magazu sun kwashi matan aure, mata da magidanta na ta barin gari domin yin gudun hijira.”

Mutumin ya kuma shaida wa BBC cewa ko a farkon watan ramadan yanbindigar sun shiga sun dauki mata gida-gida sai da aka bada miliyan hudu da dubu 300, “bayan an kai masu suka kuma nemi a saya masu mashin, kuma bayan sun sauko matan da kwana biyu suka sake dawowa suka kwashi mutane.”

Sai dai gwamnatin jihar ta danganta hakan ne da irin matsin lambar samame da jami’an tsaro ke kai wa ‘yan bindigan ta sama da kasa a maboyarsu.

Sulaiman Bala Idris, mai magana da yawun gwamnan jihar ta Zamfara, ya ce wadannan hare-hare ne irin na ramuwar gayya, “ cikin ƴan makwannin nan an kashe shugabanninsu da dama, kuma jami’an tsaro na ci gaba da kai masu farmaki kuma suna samun nasara, kuma wannan abin nan ya sanya suka fantsama suke kai hare-hare kauyuka suna kashe mutane domin su sake tada hankalin al’umma.”

Sulaiman Bala ya ce akwai zama da mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro , Malam Nuhu Ribadu ke yi da gwamnonin Arewa domin lalubo mafita.

Wannan dai wani albishir ne, kamar yadda wasu ke gani ba wai ga jama’ar jihar Zamfara kadai ba, har ma da sauran duk wasu wurare da matsalar tsaro ta zame wa karfen kafa a yankin arewa maso yammacin Najeriya, kuma suna nan cike da fatan gani a kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *