May 20, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An sako ɗaliban Kuriga da ƴanbindiga suka sace a Kaduna

2 min read

Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta bayar da rahoton cewa an sako duka ɗaliban makarantar Kuriga da ƴanbindiga suka sace.

An sace ɗaliban firamare da na sakandare su kusan 287 a makarantarsu da ke ƙauyen Kuriga a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna fiye da makonni biyu da suka wuce.

Sanarwar da gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya fitar ta ce an sako duka ɗaliban kuma suna cikin koshin lafiya.

Sanarwar ba tayi karin bayani ba game da irin matakan da aka bi wajen sako ɗaliban, sai dai gwamna Uba Sani ya nuna godiya ga shugaba Tinubu da mai bashi shawara kan tsaro da kuma sojojin Najeriya saboda irin rawar da suka taka wajen ganin an sako ɗaliban.

“Ba dare babu rana ina tattaunawa da Malam Nuhu Ribadu domin lalubo hanyoyin da za a bi wajen kubutar da daliban, kafin mu samu nasara,” in ji Uba Sani.

Galibinsu ɗaliban da aka sace ƴan shekaru biyar ne zuwa 18.

Wani malamin makarantar ta Kuriga mai suna Sani Abdullahi wanda ya kuɓuce ya bayyana cewa an sace dalibai na bangaren sakandare 187, sai kuma bangaren firamare ɗalibai 100.

Kwanaki biyu bayan sace ɗaliban, daya daga cikin ya kuɓuce, inda ya ce ƴanbindigar sun kora su kamar shanu, inda suka yi ta tafiya a cikin daji a wani lokacin kuma da sassarfa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *