May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gidauniyar Dangote zata gina manyan tituna da gadojin sama Kano

1 min read

Shugaban rukunin kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewar gidauniyarsa ta Dangote zata gina manyan tituna da gadojin sama domin saukakawa al’ ummar jihar Kano harkokin sifiri na yau da kullum.

Aliko Dangote ya tabbatar da hakan bayan ganawarsa da Gwamna jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf a fadar gwamnatin Kano.

Dangote yakara da cewar gidauniyarsa zata siyo magunguna domin rabawa al’ umma kyauta a asibitocin gwamnatin jihar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *