September 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Da dumi-dumi: Kotu Ta Bayyana Shuruddan Bada Belin Murja

1 min read

Babbar kotun jihar Kano ta amince da bada belin shahararriyar yar Tiktok din nan suna Murja Ibrahim Kunya.

A hukuncin da ya yanke a ranar Litinin, Mai shari’a Nasiru Saminu ya amince da bada belin Murja Kunya a kan kudi N500,000 tare da kawo mutane biyu da za su tsaya mata .

Daya daga cikin wanda zai tsaya mata, dole ya zama makusancin Murja Kunya na biyu kuma dole ne ya kasance yana da kadara a cikin ikon kotun.

Bayan haka, kotun ta umurci hukumar kula da asibitocin jihar Kano da kuma asibitin masu tabin hankali da su tabbatar da sallamar mai Murja bayan sun cika sharuddan belin.

Kotun ta dage zamanta zuwa ranar 16 ga Mayu, 2024 domin sauraren karar .

Kadaura

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *