May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Malaman Addinin Musulunci na kira ga gwamnatin Najeriya ta taimaka wa maniyyata hajji

3 min read

Malaman addinin musulunci a Najeriya sun soma fitowa suna rokon gwamnati kan ta dau matakin rage kudin kujerar hajjin bana bayan karin kusan miliyan biyu da ya tada hankula maniyyata.

Kiran malaman na zuwa ne kwana guda da hukumar alhazan Najeriya ta sanar da karin kudin, wanda malaman ke cewa dole a sauƙaƙawa maniyata, da basu farashin dala mai sauƙi don su sami damar zuwa sauke farali.

Shiekh Tijjani Bala Ƙalarawi na daga cikin wadanda sukayi wannan kiran, inda ya ce ya kamata Malamai su haɗu domin yi wa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu magana ya duba lamarin maniyyata.

”Mun san halin da kasa ke ciki da ma duniya, alhazan nan da za su je aikin hajji za u yi wa kasa addu’a, ina fatan malmai su hada kai, su samu shugaban kasa u gaya masa Allah da Annabi, kuma bai wa alhazan nan kudi kan farashin dala mai sauki ba zai cutar da gwamnatin tarayya ba.

“Kuma aikin Hajjin nan sau daya ne a shekara, duk abin da za a dauka abi wa mutum bai kai wanda wani zai dauk ma ka na kwana guda ba” in ji Malamin.

Ya kara da cewa Malamai su ne ruwa mai wanke dauda, su na da iko akan kowa kama daga majalisar dattawa kuma ba wai na arewa kadai ake magana ba, ana magana ne akan dukkan musulmai da ke fadin Najeriya.

Ana alakanta tsadar kujerar aikin Hajjin da yanzu ta kai kusan Naira miliyan 7, karyewar darajar Naira da karuwar darajar dalar Amurka.

Sai dai Sheikh Tijjani Bala Kalarawi ya ce batun dala da ake yi kan talakawa ta ke karewa.

Dala ta tashi ne akan talaka, ba tai tashin gwaron Zabi akan masu hali ba, talaka ne ya ken kudarsa.

“Wadannan da za su je aikin hajji da sauran bayin Allah da ba sai na yi magana akan su ba, amma idan ka ga mun yi magana to abin ya kai matakin Lahaula wala kuwwata illabillah.

Amma ‘yan majalisar wakilai da dattijai da ministoci da duk masu ba da shawara, su roki bawan Allan nan ya saukakawa alhazai omin su tafi da farin ciki su dawo da murna.”

Ya kuma ce jiragen jigilar Alhazai ‘yan kasuwa ne, idan aka sassautawa alhazai su ma za su sassauta musu, idan aka matsa su ma dole su matsa saboda kasuwanci su ke yi.

A ranar Litinin ne hukumar alhazan Najeriya ta ƙara kuɗin kujerar aikin Hajji da miliyan ɗaya da dubu ɗari tara, inda yanzu kuɗin suka koma naira miliyan shida da dubu 800 kan kujera ɗaya, ga wanda ya yi ajiya ko ya biya kudinsa tuntuni.

Sannan wadanda za su yi sabon biya kudin ya haura naira miliyan 8.

Hukumar ta ce hakan ya faru ne sakamakon tashin farashin dala wadda da ita ce ake yin kiyasin dukkanin abubuwan da maniyyata suke bukata.

Mai magana da yawun hukumar, Fatima Sanda Usara ta ce wadanda ba su fara biyan wani abu daga cikin kudin kujerar ba za su biya naira miliyan takwas, saboda lokacin da aka fitar da farashin kujerar aikin Hajjin bana dala ba ta yi tashin da ta yi ba yanzu.

Hukumar ta kuma ba maniyyata aikin Hajjin na bana wa’adin zuwa 29 ga watan nan na Maris da ake ciki domin kammala biyan kudin: ” Wadanda suka kasa biya suna da zaɓi biyu ko dai su rubuta a mayar masu da kuɗinsu ko kuma su ajiye kudin har zuwa shekara mai zuwa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *