May 19, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kwamishinan Yan Sandan Kano ya Bada umarnin Kama duk Mutumin da ya zo Neman Belin Yan daban da aka kama

1 min read

smart

Wasu fitattun ‘yandaba 22 yankin unguwar Dorayi a karamar hukumar Gwale da ke kwaryar birnin na Kano sun fada komar’ yansanda.

Wannan na zuwa yayin da aka samu fadan daba da kwacen waya da wasu batagari suka yi a yankin.

Kwamshinan ‘yansanda a Kano Mohammad Usaini Gumel ya ja kunnen masu zuwa neman belin’ yandaba a hannun ‘yansanda inda ya ce duk wanda ya zo neman belin su a kama shi.

Kwamishinan ‘yansanda na jihar ta Kano dai Usaini Mohammed Gumel a yayin taro da mazauna yankin ya tabbatar da cewa za su dauki matakin ba sani ba sabo ga duk wanda aka samu da laifi ko masu dorewa matasan gindi suna aikata taasa.

Ya kuma ba da umarnin kara yawan jami’an ‘yansanda da kayan aiki a yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *