May 20, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

wanda ya bayar da zakkar fidda kai bayan an sauko daga idi to bashi da ladan fidda kai – Iman Sani Zakariyya

1 min read

Limamin Masallacin juma’a na Jami’u Ibdurrahaman dake Unguwar Tudun Yola Malam Muhammad Sani Zakariyya ya bukaci Al’ummar Musulmi dasu tabbatar sun fitar da zakkar fidda kamar yadda Addinin Musulunci ya shinfida.

Malam Muhammad Sani Zakariyya ya bayyana haka ne a yayin hudubar sallar juma’a da ya gabatar a Masallacin dake Unguwar Tudun Yola.

Limamin ya Kuma ce ana baiwa fakirai da muskinai zakkar fidda akai.

Malam Muhammad Sani ya ce hatta masu aiki a gida sa sauran masu hidima a gida suma wajibine a fitar musu da zakkar.

A cewar Malamin ana fitar da zakkar ne kafin a sauko daga idi ko kafin Ranar sallah da dai sauransu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *