May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Marasa karfi da masu bukata ta musamman sama da 3000 ne suka amfana da tallafin abinci na uwar Gidan Shugaban hukumar tsaron farin Kaya ta Nigeria Hajiya Aisha Ibrahim Yusuf Bichi ta raba ta hannun Dr Ibrahim Abdullahi Rijiyar

2 min read

Exif_JPEG_420

Da safiyar wannan Rana ta Asabar 06 ga watan Aprilun, 2024 ne Kwamitin kula da rabon tallafin abinci na uwar Gidan Shugaban hukumar tsaron farin Kaya ta Nigeria hajiya Aisha Ibrahim Yusuf Bichi uwa Marayu Shekara ta biyar a jere tana gudanar da rabon tallafin abinci al’umma dake sassan jihar Kano.

Tallafin na yau Asabar dai shi ne tallafi na hudu a cikin wannan wata na Ramadan wanda aka gudanar a kwaryar birnin Kano.

A cikin haramar hukumar Bichi dai an gudanar da rabon sau biyu ne ga mutane 1800.

A wannan azumin na bana Hajiya Aisha ta raba tallafin sama da mutane dubu 3200 wanda suka shafi marasa karfi da masu bukata ta musamman a sassan Kano.

Shirin rabon tallafin ya kalli sassa daban-daban na jihar Kano a Unguwannin kusa da na nesa

A kwaryar birnin Kano dai Shima an gudanar da rabon tallafin sau biyu ne, inda mutane Sama da dubu 1400 suka amfana da wannan tallafi.

A dadin mutanan da suka amfana da tallafin dai a wannan Shekara idan aka hada da wanda aka gudanar sau biyu a Bichi da Kuma na Kano Shima dai biyu, mutane Sama da 3200 ne suka amfana wanda dukkansu mabukata ne .

Da yake jawabi Shugaban Kwamitin kula da rabon Dr Ibrahim Abdullahi Rijiyar ya ce hajiyar Aisha a ko da wani lokaci bata da burin da ya wuce ganin mabukata da musamman marasa galihu sun shiga cikin farin ciki kamar sau Al’umma.
Ya Kuma bukaci Wanda suka amfana dasu cigaba da Sanya Hajiya Aisha cikin addu’o’insu na yau da kullum.

A tabakin mutanan da suka amfana da tallafin kuwa, mutane sun yi murna da godiya inda wasu suka riga fadin irin halin da suke ciki na rashin abinci, kafin samun wannan taimakawo a yau.

Wani magidanci mai suna Abdul Aminu cikin kuka ya bayyana farin cikinsa, inda yayi addu’a ga mutanan da suka assasa wannan alheri dama Dakta Ibrahim Abdullahi Rijiyar lemo.

Shi kuwa Malam Abubakar Mudi cewa yayi ko yau bashi da abincin da zai ci, amma cikin taimakon Allah ta hannun Dr Ibrahim Abdullahi sun amfana da kayan abinci kala da dama a cikin buhun da aka basu.

A yayin taron an raba kayan abinci da suka Hadar da shinkafa marasa sugar Gero wake mai taliya da Kuma Makaroni .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *