May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Marasa karfi da masu bukata ta musamman sama da 3000 ne suka amfana da tallafin abinci na uwar Gidan Shugaban hukumar tsaron farin Kaya ta Nigeria Hajiya Aisha Ibrahim Yusuf Bichi wanda ta raba ta hannun Dr Ibrahim Abdullahi Rijiyar lemo

3 min read

Exif_JPEG_420

Da safiyar wannan Rana ta Asabar 06 ga watan Aprilun, 2024 ne Kwamitin kula da rabon tallafin abinci na uwar Gidan Shugaban hukumar tsaron farin Kaya ta Nigeria hajiya Aisha Ibrahim Yusuf Bichi uwar Marayu, wanda wannan Shekara ta biyar kenan a jere tana gudanar da rabon tallafin abinci ga al’umma dake sassan jihar Kano.

Tallafin na yau Asabar dai shi ne tallafi na hudu a cikin wannan wata na Ramadan a wannan shekarar wanda aka gudanar a waje da kuma kwaryar birnin Kano.

A cikin karamar hukumar Bichi dai an gudanar da rabon sau biyu ne ga mutane 1800.

A wannan azumin na bana Hajiya Aisha ta raba tallafin ga mutane 3100 wanda suka shafi marasa karfi da masu bukata ta musamman a Jahar Kano.

Shirin rabon tallafin ya kalli sassa daban-daban na jihar Kano a Unguwannin kusa da na nesa

A kwaryar birnin Kano dai Shima an gudanar da rabon tallafin sau biyu ne, inda mutane Sama da dubu 1200 suka amfana da wannan tallafi.

A dadin mutanan da suka amfana da tallafin dai a wannan Shekara idan aka hada da wanda aka gudanar sau biyu a Bichi da Kuma na Kano Shima dai sau biyu, mutane Sama da 3100 ne suka amfana wanda dukkansu mabukata ne .

Da yake jawabi Shugaban Kwamitin kula da rabon Dr Ibrahim Abdullahi Rijiyar ya ce hajiya Aisha a ko da wane lokaci bata da burin da ya wuce ganin mabukata da marasa galihu sun shiga cikin farin ciki kamar sauran Al’umma.
Ya Kuma bukaci Wanda suka amfana dasu cigaba da Sanya Hajiya Aisha cikin addu’o’insu na yau da kullum.

Dakta Ibrahim ya Kuma bukaci Al’ummar dasu cigaba da Sanya Mai gidanta a cikin Addu’o’i Allah ya bashi nasara a aikin sa, ya kareshi daga dukkan sharri, Allah ya yi Albarka ga ziri’arsu baki daya.

A tabakin mutanan da suka amfana da tallafin kuwa, mutane sun yi murna da godiya inda wasu suka ringa fadin irin halin da suke ciki na rashin abinci, kafin samun wannan taimakon a yau.

Sun Kuma yi Addu’a ta musamman ga Alhaji Yusuf Bichi da hajiya Aisha kan cewa Allah ya karesu baki daya.

Sun Kuma ce Hajiya Aisha da Alhaji Yusuf Bichi sun chanchanci addu’o’i na musamman ga dukkan Wanda suka amfana da tallafin munji dadi sosai.

Wani magidanci mai suna Abdul Aminu cikin kuka ya bayyana farin cikinsa, inda yayi addu’a ga mutanan da suka assasa wannan alheri wato Hajiya Aisha.

Ya ce mun gode mun gode Allah ya sa a dauka a gidan Aljannar fiddausi.

Shi kuwa Malam Abubakar Mudi cewa yayi a yau bashi da abincin da zai ci, amma cikin taimakon Allah sai ga tallafin buhun abinci daga Hajiya Aisha ya samu ta hannun Dr Ibrahim R/lemo.

A yayin taron an raba kayan abinci da suka Hada da: Shinkafa Masara Sugar Gero Wake Taliya Makaroni da Kuma Man girki .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *