May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Wasu Masu karamin karfi sun bayyana godiya ga uwar marayu da marasa galihu Hajiya Aisha Yusuf Bichi bisa tallafin kayan abinci ta hannun Dr Ibrahim Abdullahi Rijiyar lemo

1 min read

Exif_JPEG_420

Da safiyar wannan Rana ta Asabar ne Kwamitin kula da rabon tallafin abinci na uwar Gidan Shugaban hukumar tsaron farin Kaya ta Nigeria hajiya Aisha Yusuf Bichi ta gudanar da rabon tallafin abinci ga Marayu da marasa galihu dake Unguwannin Kano domin rage musu fatara da yunwa.

Tun da fari dai Shugaban kula da rabon Dr Ibrahim Abdullahi Rijiyar lemo ya bayyana cewa wannan shi ne karo na hudu da akai Rabon a nan kwaryar Kano, inda ya ce anyi rabo na biyu a Karamar hukumar Bichi.

Ta cikin bayaninsa ya bukaci Al’ummar Musulmi da suka amfana da su cigaba da yiwa Hajiya Aisha Bichi Addu’a da ita da mai gidanta da sauran Yan uwa.
.
wasu daga cikin mutanan da suka amfana da tallafin abinci sun bayyana farin cikin su tare da godiya ga uwar Marayu da marasa galihu.

A yayin taron an raba kayan abinci da suka Hadar da shinkafa marasa sugar Gero wake mai taliya da Kuma Makaroni .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *