May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mutum fiye da 2000 sun mutu a wata uku a Najeriya – Rahoto

2 min read

Wani rahoton da kamfanin tsaro na Beacon Consulting da ke Abuja ya fitar a makon nan ya nuna yadda ‘yan Najeriya 2,200 suka mutu sakamakon matsalolin tsaro sannan aka yi garkuwa da mutum 2,270.

Rahoton ya alakanta kisan jama’a da hare-haren ‘yan ta’adda da masu satar jama’a da kuma ayyukan dakarun tsaro na gwamnati da na sa-kai.

Shugaban kamfanin, Malam Kabiru Adamu ya shaida wa BBC cewa kaso fiye da 90 na alkaluman na mace-macen da sace-sacen duka a arewacin Najeriya musamman arewa maso yammaci.

Ya kara da cewa a watan janairun wannan shekarar mun samu mutum fiye da 1000 da aka kashe, inda a watan biyu kuma aka samu fiye da 700 sannan a Maris din da ya gabata aka samu fiye da 800.

“Mun sami wadanda suka mutum mutum 855 a watan farko, a watan biyu kuma 747 ka ga kenan an samu karin 8.71 a cikin 100. Ka ga kenan mun samu mutum dubu biyu da dan wani abu a kai kenan.”

Dangane kuma da wadanda aka yi garkuwa da su Malam Kabiru ya ce “idan kuma ka zo batun garkuwa domin kudin fansa mun samu mutum 2270.”

To sai dai ya bayar da hanyoyin da idan aka bi su to za a kai ga gaci.

“Dole ne a samu hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnoni musamman na arewa.” In ji Malam Kabiru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *