May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

APC ta dakatar da Abdullahi Ganduje a matakin mazaɓa

2 min read

APC ta dakatar da Abdullahi Ganduje a matakin mazaɓa Jam’iyyar APC reshen mazaɓar Ganduje da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano ta dakatar da shugaban jam’iyyar naa ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje nan take. Mai bai wa jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a a mazaɓar Ganduje ne Haladu Gwanjo ya sanar da dakatar da shugaban jam’iyyar a wani taron manema labarai da aka yi a Kano ranar Litinin. Gwanjo ya bayyana cewa matakin dakatar da Ganduje daga jam’iyyar ya faru ne saboda zargin da gwamnatin Kano take masa na aikata rashawa da wadaƙa da kuɗaɗe. A cewarsa, mambobin jam’iyyar sun yanke shawarar dakatar da shugaban APC na ƙasa ne bayan ƙuri’ar yanke ƙauna da aka kaɗa a kan shi saboda gazawarsa wajen wanke sunansa daga tarin zarge-zargen da aka yi masa na rashawa da cin hanci. Zarge-zargen dai sun haɗa da wani bidiyo da aka yi ta yaɗawa wanda a ciki ake zargin sa da karɓar cin hanci daga ɗan kwangila. Gwanjo ya bayyana cewa matakin ya fara aiki daga yau ɗin nan – 15 ga watan Afrilu. Sai dai bayanai na nuna cewa ba a yi sallamar da yawun shugaban jam’iyyar mazaɓar ba.

Jam’iyyar APC reshen mazaɓar Ganduje da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano ta dakatar da shugaban jam’iyyar naa ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje nan take.

Mai bai wa jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a a mazaɓar Ganduje ne Haladu Gwanjo ya sanar da dakatar da shugaban jam’iyyar a wani taron manema labarai da aka yi a Kano ranar Litinin.

Gwanjo ya bayyana cewa matakin dakatar da Ganduje daga jam’iyyar ya faru ne saboda zargin da gwamnatin Kano take masa na aikata rashawa da wadaƙa da kuɗaɗe.

A cewarsa, mambobin jam’iyyar sun yanke shawarar dakatar da shugaban APC na ƙasa ne bayan ƙuri’ar yanke ƙauna da aka kaɗa a kan shi saboda gazawarsa wajen wanke sunansa daga tarin zarge-zargen da aka yi masa na rashawa da cin hanci.

Zarge-zargen dai sun haɗa da wani bidiyo da aka yi ta yaɗawa wanda a ciki ake zargin sa da karɓar cin hanci daga ɗan kwangila.

Gwanjo ya bayyana cewa matakin ya fara aiki daga yau ɗin nan – 15 ga watan Afrilu.

Sai dai bayanai na nuna cewa ba a yi sallamar da yawun shugaban jam’iyyar mazaɓar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *