May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mun gabatar da tuhume-tuhume takwas kan Ganduje – Muhuyi Magaji

2 min read

Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimin Gado ya ce sun suna yi wa tsohon gwamnan jihar Kano kuma shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje tuhume-tuhumen guda takwas.

A cewar Muhuyi tuhume-tuhumen sun haɗa da waɗnda suka danganci shigar kuɗi kimanin naira miliyan ɗari shida daga asusun gwamnatin Kano zuwa wani kamfani “wanda tsohon gwamna yake darakta a wajen sannan wanda yake tasarrafi da asusun mai ɗakinsa ce take yi”

Nan gaba a yau Laraba ne dai ake sa ran za a fara sauraron ƙarar da gwamnatin Kano ta shigar kan tsohon gwamnan jihar da iyalansa da wasu makusantansa bisa zargin cin hanci da rashawa da almundahana da dukiyar al’umma.

A na sa ran a gudanar da zaman fara sauraron shari’ar ne ƙarƙashin mai shari’a Usman Na’abba na babbar kotu mai lamba huɗu da ke jihar.

Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimin Gado ya ce akwai ƙari cikin waɗanda ake ƙara da suka haɗa da mutum huɗu da wasu kamfanoni.

A cewarsa, sun shirya gabatar da shaidu 15 da za su gabatar gaban kotu saboda “mun samo hujja da ta danganta tsohon gwamna da laifuffuka da dokar hukuma ta haramta.”

Muhuyi Magaji ya ce akwai tuhume-tuhume takwas da suke yi kan tsohon gwamna Ganduje.

Sai dai wasu na ganin matakin gurfanar da tsohon gwamnan Kano da iyalinsa da hukumar yaƙi da rashawa ta jihar Kano ke yi masu yunƙuri ne na ramuwar gayya kan dakatarwar da Ganduje ya yi wa shugabanta – Muhuyi Magaji, zargin da ya musanta.

Ya bayyana cewa “shi ne dalilin da ya sa aka dakatar da ni tun farko, abu ne da muka fara shi tun yana gwamnati kuma ƴan jarida sun faɗa muna bincike kan wasu abubuwa da iyalinsa suke, kuma su ba su ƙaryata ba, babu wanda ya fito daga gwamnati ya ƙaryata,”

“Kuma abin da aka ce an dakatar da ni a kan shi, ba a iya tabbatar da shi ba har kotu ta ce mu dawo.” a cewar Muhuyi.

Ya ce akwai ƙarar da ke gabansu “wadda muka gano kuɗin ƙananan hukumomi, naira miliyan dubu 51 da miliyan 300.”

Game da wannan zargi na Muhuyi Magaji, lauyan tsohon gwamna Ganduje, Barista Musa Lawan ya ce ba za su halarci zaman kotun ba saboda har izuwa lokacin da BBC ta tattauna da shi, ya ce ba su samu takardar gayyata ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *