May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

EFCC na neman tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello ruwa a jallo

1 min read

Hukumar yaƙi da cinhanci a Najeriya EFCC ta ayyana tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.

Matakin hukumar na zuwa ne ‘yan awanni bayan kotu ta ɗage sauraron ƙarar da hukumar ta shigar saboda wanda take zargin bai halarci zaman kotun ba.

Yayin zaman kotun na ranar Alhamis, lauyan EFCC mai suna Kemi Phinro ya faɗa mata cewa “wani mutum da ke da kariya daga tuhuma ne ke bai wa tsohon gwamnan mafaka”.

“EFCC na tuhumar Yahaya Bello da zargin halasta kuɗin haram da suka kai naira biliyan 8.2,” in ji hukumar cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na zumunta ɗauke da hoton tsohon gwamnan.

Tun a jiya Laraba rahotonni suka ce gwamnan Kogi na yanzu Usman Adodo ne ya fice da Yahaya Bello a motarsa lokacin da jami’an EFCC suka yi wa gidansa tsinke a Abuja.

Gwamnatin Kogi ba ta ce komai ba game da zargin.

Lauyan hukumar ya kuma ce suna duba yiwuwar neman taimakon rundunar sojin Najeriya wajen kamawa tare da gurfanar da shi a gaban kotun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *