May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Wani magidanci a Kano ya kashe matarsa da dutsen guga

1 min read

Kotun majistre mai lamba 26 ta aike da wani magidanci Adamu Ibrahim gidan yari bisa zarginsa da hallaka mai matarsa ta hanyar buga mata dutsen guga a fuska.

Lamarin ya faru ne a garin Kwanar Dangora da ke karamar hukumar Kiru ta Jihar Kano.

Acewar Adamu sabani ne ya shiga tsakaninsa da matarsa dalilin wata mata da ta nuna ba ta son mu’amalarsa da ita.

Sai dai ya ce ya yi ƙoƙarin fahimtar da ita, amma abin ya ci tura, inda ta ce babu ita babu zama da kishiya.

Daga nan ne a cewarsa ta kama shi da kokawa, kuma duk da ihun da yake yi ta ki rabuwa da shi, har ya aikata abinda ya aikata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *