May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Al’ummar karamar hukumar Ungoggo sun ya bawa Gwamnatin Kano wajen kula da harkokin kiwon lafiya a fadin jihar Kano

2 min read

Gwamnatin Kano ta jaddada aniyar ta wajen cigaba da baiwa harkokin kiwon lafiya kulawa ta musamman.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dr Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bayyana haka, a yayin kaddamar da allurar riga-kafin polio a karamar hukumar Ungoggo.

Kwamishinan ya ce, a iya lokacin da suka karfi mulki a daga hannun tsohuwar Gwamnati, Gwamnatin Kano ta gudanar da ayyuka sababbi da dama wanda al’umma sun shaida hakan.

Ya kara da cewa Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf a ko da yaushe burinta shi ne ganin ta baiwa Ma’aikatar kula wajen ganin an kula da lafiyar al’umma musamman ma ƙananan yara.

Ya kuma bukaci iyaye dasu cigaba da kai yaransu allurar riga-kafin polio domin kare kananan Yara da kamuwa daga ko wata irin cuta.

Wasu daga cikin al’ummar yankin na Ungoggo sun bayyana farin cikin su, tare da godiya ga Allah bisa samun wannan Gwamnati mai kishin talakawa.

Sun kuma roki Gwamnan da ya cigaba da baiwa bangaren lafiya gudunmawa kamar yadda yake yi a halin yanzu.

Shugaban kwamitin riko na Karamar hukumar Ungoggo Sani Abdullahi Ungoggo ya bukaci iyaye musamman mata dasu tabbatar sun fito da ƴaƴansu wajen allurar riga-kafin ta polio.

Ya kuma ce karamar hukumar zata sanya ido wajen an gudanar da aikin cikin nasara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *