May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An rufe makarantar da ɗalibai suka ci zalin wata yarinya a Abuja

3 min read

Masu amfani da kafofin sa da zumunta sun ringa yada bidiyon suna neman a dauki mataki kan cin zarafin dalibar ta makarantar Lead British International School, yayin da maudu’in cin zalin ya kasance cikin wadanda suka fi daukar hankali a Nijeriya, kamar yadda kamfanin dallancin labarai na TRT Afrika Hausa ya wallafa.

Hukumomin makarantar sun ce sun kaddamar da bincike kan cin zarafin dalibar.

Hukumomin wata makarantar sakandare mai zaman kanta a Abuja babban birnin Nijeriya, Lead British International School sun sanar da rufe ta har na tsawon kwana uku, sakamakon rikicin da ya tayar da ƙura na “cin zalin wata yarinya da wasu ɗalibai suka yi.”

Wannan na zuwa ne bayan da wani bidiyo da aka nuna ɗaliban na cin zalin yarinyar, wadda ita ma ɗaliba ce ta hanyar dukanta ya karaɗe shafukan sada zumunta, tare da jawo Allah-wadai da kiraye-kirayen neman hukumar makarantar ta ɗauki mataki.

A sanarwar da hukumomin makarantar suka yi a wani bidiyo da aka yaɗa a shafukan masu faɗa a ji na Instagram a tanar Talata, an ga wani jami’in makarantar yana cewa an rufe ta bisa buƙatar da Ma’aikatar Mata ta Nijeriya ta nema na yin hakan.

“Bisa buƙatar Ministar Mata ta Nijeriya, kuma da yake mu ƴan Nijeirya ne da muke girmama doka da oda kuma a ƙarƙashin doka muke aiki. Saboda makarantarmu fitacciya ce kuma an yi mata rajista ƙarƙashin hukumar babban birnin Nijeriya Abuja, a don haka, daga yau an rufe Lead British International School, Abuja, tsawon kwana uku,” in ji mutumin.

Tayar da ƙura

Tun da fari dai a ranar Litinin ne masu amfani da kafofin sada zumunta a Nijeriya suka ringa yaɗa wani bidiyo da aka ga ɗaliban makarantar ta Lead British suna cin zalin wata ɗaliba ta hanyar dukanta.

A bidiyon, an ga ɗalibar sanye da kayan makaranta, yayin da wasu ɗaliban mata biyu suka tsaya a kanta suna kwaɗa mata mari, sannan wani ɗalibi namiji yana zaune a gefe yana dariya, sai kuma wasu ɗaliban da ake jiyowa suna zuga masu marin, yayin da ita wadda ake marin ta gaza yin kataɓus.

A ɗaya bidiyon kuma an gan su a wata baranda ta saman makarantar da alama sun tare yarinyar suna dukanta.

Shafuka da dama musamman a Instagram sun yi ta saka bidiyoyin tare da yin kira ga hukumomi da su shiga maganar, inda dubban mutane suka yi ta tsokaci suna bayyana ra’ayoyinsu, waɗanda mafi yawa caccakar yaran da aka ga sun aikata laifin ake yi.

Daukar mataki

Dama tuni makarantar ta ce ta kafa kwamiti da zai binciki tare da ɗaukar mataki kan zargin cin zarafin dalibar da takwarorinta dalibai suka yi.

A cikin wata sanarwa da makarantar ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Talata ta ce ta damu da abinda ya faru, sannan tana daukar batun da matukar muhimmanci.

A sanarwar da Lead British International School ta fitar ta ce ta kwafa kwamitin da zai bincika batun, kuma tuni ya fara aiki tare da tattara bayanai da kallon bidiyon cin zarafin.

Ta ƙara da cewa za a taimaka wa yarinyar da aka ci zarafin nata tare da iyayenta ta hanyar ba su shawarwari da kuma duk wani tallafi da ya kamata.

Sannan makarantar ta ce su kuma daliban da suka ci zarafin takwarar tasu, “za mu yi aiki tare da su da iyayensu, za a ba su shawarwari da kuma ladabtar da su don hana faruwar irin hakan a gaba.”

Ba yau farau ba

Ba wannan ne karo na farko da aka fara samun zargin cin zalin ɗalibai ba a makarantu a Nijeriya, an kai matakin da ake ganin abin ya zama ruwan dare, inda a wasu lokutan yakan fito daga malamai a kan ɗalibai ko kuma ɗalibai su ci zalin ɗalibai ƴan’uwansu.

Na bayan nan da ya faru har ya tada ƙura a ƙasar shi ne na watan Disamban 2021 inda wani ɗalibi a makarantar Dowen College Lagos, mai shekara 12, Sylvester Oromoni ya rasa ransa sakamakon zargin cin zalinsa da wasu ɗalibai suka yi.

Rahotanni sun ce ɗaliban sun yi wa Oromoni duka ne wanda daga baya ya yi ajalinsa. Sai dai hukumar makarantar ta ƙaryata zargin a lokacin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *