May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An janye wa Muhuyi ƴansandan dake tsare hukumar

2 min read

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta yi ƙarin haske game da janye jami’an ƴan sandan da ke samarwa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano tsaro inda ta ce an ɗauki matakin ne saboda za a yi aikin tantance yawan ƴan sandan da ke ƙarƙashin hukumar da kuma fahimtar yanayin ayyukansu tun 2015 da aka tura su yin aiki a hukumar.

Bayanin na ƙunshe cikin sanarwar da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar inda ta ce za a tantance su ne bayan rahotannin da aka samu ta hannun sashen karɓar ƙorafe-ƙorafe na rundunar da ke nuna cewa ana amfani da ƴan sandan da ke aikin samar da tsaro a hukumar wajen cimma wasu ƙudurori da ba aikinsu ba.

Sanarwar ta ce akwai buƙatar mutane su fahimci cewa ana tantance ma’aikatan domin martani ga rahotannin da kafafen yaɗa labarai ke watsawa.

Matakin, a cewar sanarwar, ya zama wajibi domin gyara matsalolin da aka gano game da yadda hukumar ke gudanar da ayyukanta ganin cewa ana amfani da ƴan sandan da aka tura su samar da tsaro wajen yin kame da gudanar da bincike kan ƙararraki, wanda ƙarara ya nuna cewa sun sauka daga tsarin gudanar da aikin da ya rataya a wuyansu – wani abu da ya zama dole a yi gyara a kai.

Rundunar ta ce a baya ma an gudanar da irin wannan aikin tantance ƴan sandan daga lokacin da aka kafa hukumar a 2015 kuma ƴan sandan suka koma bakin aiki bayan kammala aikin.

Sanarwar ta ce babban sufeton ƴan sanda ya umarci ƴan sandan da aka gama tantancewa su gagauta komawa bakin aiki.

Kazalika rundunar ta ce idan har hukumar na son ƙarin jami’an ƴan sanda da za su yi mata wasu ayyukan da ba sa cikin waɗanda babban sufeton ya amince, hukumar na iya neman izini daga shugaban ƴan sandan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *