May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ana cigaba da fargaba bayan Gini mai hawa biyu ya rufta kan magina fiye da 15 a unguwar Kuntau

1 min read

Ana fargabar wani gini mai hawa biyu da ya ruguje ya faɗa kan wasu magina da ake aikin gini a yankin Kuntau da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano.

Wata majiya ta tabbatar wa BBC cewa ginin ya rufta kan magina fiye da 15.

Tuni dai masu aikin ceto suka fara zaƙulo mutanen da suka maƙale a ginin.

Zuwa lokacin da Bustandaily ke haɗa wannan rahoto, an zaƙulo mutum uku sai dai ɗaya a cikinsu ya mutu yayin da biyun ke cikin mawuyacin hali.

Kawo yanzu dai ba a tantance adadin mutanen da ibtila’in ya rutsa da su ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *