May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Yan Sanda a Kano sun gano muggan kayan maye a daddaure a Ledoji sai kuma Takobi da Adduna

1 min read

Rundunar Yan Sandan Jahar Kano, ta samu nasarar Kai sumame a yankin Hadejia road, tare da gano wasu muggan kayan maye a daddaure a Ledoji sai kuma Takobi da Adduna.

Kakakin Rundunar Yan Sandan Jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne, ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook.

SP Abdullahi Kiyawa, ya ce wadanda ake zargi da mallakar kayan, sun cika wandunansu da iska, amma suna ci gaba da farautarsu.

Sai dai ya shawarci ma su kayan da su Kai Kansu Helkwatar Rundunar Yan Sandan dake Unguwar Bompai, ko kuma duk Wanda ya San inda suke ya taimaka wa Rundunar Wajen bata Bayanan sirri domin Kamo su, ko a Kira wannan lambar 08036379054, don sanar da ita.

📸Facebook/Abdullahi Haruna Kiyawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *