May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Rundunar Yan sandan Kano ta musanta labarin da Gwamnatin Kano ta fitar na cewa karfe ne ya fadowa Dan jarida ba Harbin bindiga ba

1 min read

Wannan bayani da rundunar yan sandan ta fitar ya musanta ikirarin gwamnatin Kano cewar wani karfe ne daga gini da ake yi a fadar gwamnatin ya raunata ɗan jaridar.

Mai magana da yawun gwamnan Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa a sanarwar da ya fitar ya musanta cewa harsashine, to sai dai rundunar yan sanda ta tabbatar da batun harsashin

Kwamishinan ƴan sandan Kano CP Muhammad Hussaini Gumel a tattaunawarshi da kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya tabbatar da cewa harsashine ya raunata ɗan jaridar, amma sun bincika bindigogin jami’an ƴan sandan dake aiki a fadar gwamnati kuma babu wani harsashi da ya fita daga cikinsu.

Hakan na nuna cewar harsashin daga wani wurin ya dira a fadar gwmanatin Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *