May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Biyo bayan kalaman Kwamishinan Ilimi mai zurfi na Kano Malaman Kwalejin sun rufe Kwalejin a wani mataki na mayar da martani

1 min read

Ƙungiyar malaman kwalejin shari’a ta Malam Aminu Kano (Legal) ta dakatar da rubuta jarrabawar da daliabai ke yi tare da rufe makarantar.

Daukar matakin ya biyo bayan kalaman da kwamishinan ilimi mai zurfi Dr. Yusuf Ibrahim Kofar Mata ya wallafa shafinsa na Facebook dake nuna rashin goyan bayan cire kalmar “Islamic” daga cikin sunan makarantar.

Cire kalmar dai na daga cikin ka’idojin da za’a cika kafin a daga likafar makarantar zuwa kwalejin ilimi wato College of Education.

Abin jira a Gani dai matakin da Gwamnatin Kano zata dauka kan lamarin kasancewar Makarantar nada tarihin gaske wanda akwai bukatar kara bunkasa cigaban ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *