May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Muna kira ga Gwamnati ta daga likkafar Kwalejin Shari’a da Addinin Musulunci ta Legal zuwa matakin Kwalejin Ilimi – Malam Muhammad Sani Zakariyya

2 min read

Malaman Addinin Musulunci a nan Kano sun bukaci Gwamnati data mayar da data dauka na karawa kwalejin Shari’a da Addinin Musulunci ta Aminu Kano girma zuwa matakin Kwalejin Ilimi domin Ganin irin muhimmancin da wannan Makaranta take dashi ga cigaba musamman Kara bunkasa cigaban matasa masu tasowa a nan Kano.

Guda daga cikin limaman Addini Kuma limamin Masallacin juma’a na Jami’u Ibdurrahaman dake nan Kano Malam Muhammad Sani Zakariyya ne yayi wannan kira ta cikin Hudubar sallar juma’a da ya gudanar a Masallacin na Ibdurrahaman dake Unguwar Tudun Yola.

Limamin ya bukaci Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da ya tabbatar da ganin Kwalejin ta samu wannan matsayi, wanda hakan ne zai zama cigaba ga Al’umma jihar Kano baki daya.

Malam Muhammad Sani Zakariyya ya Kuma bukaci al’umma da sauran masu ruwa da tsaki musamman ma a bangaren ilimi dasu yi dukkan iya kacin iyarsu domin sanarwa da Kwalejin wannan cigaba.

Akan ganin Legal ta fara gudanar da Digiri a Kwalejin a dazu ma sai da Ƙungiyar malaman kwalejin shari’a ta Malam Aminu Kano (Legal) ta dakatar da rubuta jarrabawar da daliabai ke yi tare da rufe makarantar.

Daukar matakin ya biyo bayan kalaman da kwamishinan ilimi mai zurfi Dr. Yusuf Ibrahim Kofar Mata ya wallafa shafinsa na Facebook dake nuna rashin goyan bayan cire kalmar “Islamic” daga cikin sunan makarantar.

Cire kalmar dai na daga cikin ka’idojin da za’a cika kafin a daga likafar makarantar zuwa kwalejin ilimi wato College of Education.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *