May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Harkar kiwon lafiyar Al’umma ba Abu bane da za’ayi wasa dashi ba – Hakimin Gwale Alhaji Yahaya Inuwa Abbas

3 min read

Dan Lawan din Kano Hakimin Gwale Alhaji Yahaya Inuwa Abbas, ya bukaci Daliban bangaren Community Health dake nan Kano dasu sanya tsaron Allah da kishin kasa dama jihar Kano a dukkan inda suka tsinci kansu.

Exif_JPEG_420

Exif_JPEG_420

Exif_JPEG_420

Alhaji Yahaya Inuwa Abbas ya bayyana haka ne a yayin taron baiwa Daliban community Health na Makarantun koyar da harkokin kiwon Lafiya masu zaman kansu guda Bakwai wanda ya gudana a Makarantar Emirates College of Health Sciences and Technology dake Unguwar Tudun Yola Kabuga a nan Kano.

Hakimin ya kara da cewa duk wanda ya taimaki marasa lafiya, yayi aikin bisa tsaron Allah to tabbas Allah zai sanya masa lada mai yawa.

Ya Kuma kara da cewa do ne su kare duk wani sirri na maralafiya kasancewa na cikin amanar aikin su tun kafin su fara gudanar da aikin su.

Ya Kuma ya bawa Makarantun bisa wannan kokari da sukai na hade kansu guri guda domin Samar da cigaba musamman bangaren lafiya mai matukar muhimmanci.


Da yake jawabi Daraktan Makarantar Emirates college of health sciences and Technology, Garkuwar Marayu da marasa galihu Dr Sha’aibu Sulaiman wanda Makarantar sa ce, ta karbi bakwancin taron ya bayyana godiyar sa, ga Makarantu bakwai bisa hadin haduwa guri daya tare da bada dukkan gudunmawar da ta kamata domin ganin an gudanar da taron cikin nasara da kwanciyar hankali.

Dr Sha’aibu ya kara da cewa wadannan daliban Makarantu sun kammala karatun su, na bangaren Community Health tun Shekara ta 2023 wanda a yau Asabar ne ake rantsar dasu tare da masu takardar tabbatar da shaidai kwarewa.

Darakta ya Kuma ya bawa dukkan Malaman Emirates college tun daga kan masu kula da tsaro na Makarantar bisa gudunmawar da suka bayar wajen ganin an gudanar da taron lafiya batare da wata matsala ba.

Ya Kuma jinjinawa Jami’in hulda da jama’a na Emirates College Abdulkabir Sulaiman bisa kokarinsa na jajircewa a ko da yaushe babu dare babu Rana.

Daraktan ya Kuma ce aikin lafiya da karatun lafiya yana da Banbamci da sauran bangarori kasancewar rayuwar mutane ce ake lura da ita , a dan haka wajibine abi ka’idojin da aka shinfida domin gudun Cutar da Al’umma.

Sai dai ya ja hankalin malaman Emirates dasu cigaba dagewa wajen cigaba da kula da aikin su, kasancewar duk lokacin da aka yabamaka to tabbas sai an sake dagewa.

Exif_JPEG_420

Exif_JPEG_420

Shima da yake nasa jawabin jami’in hulda jama’a na Emirates College of Health Sciences and Technology Abdulkabir Sulaiman ya bayyana godiyarsa ga Allah bisa nasarorin da Emirates take samu a ko da yaushe.

Ya kuma Kara da cewa cikin Daliban Makarantu bakwan da aka gudanar da wannan taro, dalibai biyu da suka fito daga Emirates su ne suka fi kowa mataki a jarabawar da akai ta Kasa, wanda wannan abin alfahari garesu.

Buhari Bashir Sani wanda shi jami’in dake kula da harkokin kudi a Emirates College of Health Sciences and Technology Kano, ya bayyana sakon bangajiya ga dukkan bakin da suka halarci taron musamman iyayen Daliban wadannan Makarantu Bakwai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *