May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An kaddamar da Sabon mai horos da Kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles

1 min read

Cikin wadanda suka halarci gabatar da sabon mai horarwar Finidi Gorge har da ministan wasanni Senator John Owan Enoh da shugaban hukumar kwallon kafa ta kasa Ibrahim Musa Gusau .

Finidi George mai shekaru 52, ya shafe watanni 20 a matsayin mataimakin Jose Paseiro da aka sallama a baya.

Ya bugawa Najeriya wasanni 62 ciki har da daukar gasar cin kofin Afirka da kuma halartar gasar cin kofin duniya sau biyu.

To sai dai babu wata sanarwa da ke nuna hukumar kwallon kafa ta kasa NNF ta sanar da kwantaragin shekarau nawa George zai shafe a matsayin mai horar wa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *