June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Cikekken bayanin gyaran dokar kafa Masarautun Kano

3 min read

Majalisar dokokin jihar Kano ta gabatar da batun yin gyara ga dokar da ta raba masarautar Kano zuwa gida biyar wadda aka aiwatar a shekara ta 2019.

Majalisar ta ɗauko batun gyaran dokar ne bayan shugaban masu rinjaye, Lawan Hussaini Dala ya gabatar da ƙudurin a zauren majalisar, a ranar Talata.

A tattaunawar sa da BBC, shugaban masu rinjayen na majalisar dokokin jihar Kano, ya ce : “Mun buƙaci a kawo dokar gaban majalisa domin yi mata gyare-gyare”.

Ya ƙara da cewa “gobe ko jibi za mu yi karatu na biyu na wannan doka a zauren majalisa.”

“Wannan na daga cikin alƙawari da jagoranmu ya faɗa”.

Dama dai wadansu ƙungiyoyi sun yi kira ga majalisar da ta duba dokar, tun bayan da jam’iyyar NNPP ta karɓi mulkin jihar a babban zaɓen Najeriya na 2023.

A shekara ta 2019 – lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje – majalisar dokokin jihar ta yi wa dokar masarautar Kano garambawul, inda ta bayar da damar rarraba masarautar ta Kano zuwa gida biyar.

A lokacin ne aka samar da sabbin masarutu huɗu, wato Rano da Karaye da Gaya da Bichi, tare da naɗa sarki mai daraja da ɗaya a kowace masarauta.

Majalisar a yanzu ta ce za ta sake dawo da dokar tare da yi mata gyaran fuska bayan zargin cewa an yi ta ne “ba bisa ka’ida ba kuma ba da kyakkyawar niyya ba.”

Ko a kwanakin baya an ruwaito jagoran jam’iyyar NNPP mai mulkin jiha ta Kano, Rabiu Musa Kwankwaso na cewa akwai yiwuwar sake duba dokar ta da ta kafa sabbin masarautun na Kano.

Cikin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a jihar ta Kano, Rabiu Kwankwaso wanda ake wa kallon shi ne uba a gwamnatin Abba Kabir Yusuf ya ce an kafa masarautun ne da wata niyya ta daban wadda ba ta dace ba.

An tambayi Kwankwaso ko mai zai iya cewa game da lamarin masarautun jihar Kano, sai ya ce “Gaskiya yana ɗaya daga cikin abubuwan da ba a taɓa zama da ni a kai ba, amma kuma nasan dole za a zo a yi magana.”

“A duba a ga abin da ya kamata a yi a kai, gyara za a yi ko rusau za a yi,” in ji Kwankwaso.

Tsohon gwamnan ya ce “ai gyara za a yi a kai” a don haka dole za a yi nazari kan dokar.

Tanadin dokar masarautun Kano
Dokar ta yi tanadi 51, kamar yadda majalisar dokokin jihar Kano ta bayyana a lokacin da ta yi wa dokar gyara a shekara ta 2019.

Ga wasu muhimmai daga cikin su.

Gwamna ne zai zabi shugaban majalisar sarakuna da za a kafa nan gaba
Gwamna ne zai nada masu zabar sarki a duk lokacin da bukatar hakan ta taso
Duk sarkin da gwamna ya zaba don shugabantar majalisar sarakuna, zai jagoran ce ta ne tsawon shekaru biyu
Duk sarkin da ya ki halartar tarukan majalisar sarakunan har sau uku ba tare da kwakkwaran dalili ba, ya kori kansa daga sarauta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *