June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Za’a dauki tsahon sati daya ana yi wa yara gwajin cutar tarin fuka a Kano – Dr Abubakar Labaran

2 min read

Kwamishinan Lafiya na jihar Kano, Dr. Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gudana a ranar Litinin, a wani ɓangare na tunawa da ranar gwajin tarin TB na duniya da yake gudana a duk ranar 27-5-2024.

Dakta ya ce, za a yi sati guda ana aiwatar da wannan gwaje-gwaje, wanda baya ga gwajin cutar Tarin Fuka za a kuma yi gwajin cutar ƙanjamau da cutar cutar yunwa (Tamowa) da gwajin hoto.

Ya ƙara da cewa, za a shiga makarantu da tsangayu domin a tabbatar an yi wa kowane yaro gwajin kyauta.

A cewarsa, “Akwai rigakafi da za a yi na yara masu gararamba a gari da waɗanda suke a gidajen gajiyayyu da gidajen Marayu.

“Tarin Fuka, tari ne da ake ɗaukar sa ta hanyar iska saboda ƙarancin garkuwar jiki, kuma duk yaron da bai je an tantance shi ba an ba shi magani ba, akwai yiwuwar ya sanya wa yara 10 zuwa 15 wannan tari a cikin shekara ɗaya.

Exif_JPEG_420

Al’ummar jihar Kano ta sani kowane ɗa yana da haƙƙin a tantance shi a tabbatar ba shi da wannan cuta. Haka kuma, kowane Uba yana da haƙƙi na ya kai ɗansa ko ƴarsa inda ake tantance waɗannan cututtuka,” inji Dr. Labaran.

A darshe, ya yi wa Gwamnatin Tarayya hodiya da ta bai wa jihar Kano injinan da ake ɗaukar jini guda 20 da sauran kayayyakin aiki, ya kuma yaba wa Gwamnatin Kano da sauran ƙungiyoyin da suke tallafa wa harkar lafiya a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *