July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Rikicin Sarautar Kano: Kotu Gwamnatin Kano ta biya Sarki Aminu Ado Bayero Diyyar Naira miliyan 10

2 min read

Babbar Kotun Tarayya mai lamba 3 dake zaman ta a Kano, karkashin jagorancin mai Shari’a Simon Amobeda, ta umarci gwamnatin jihar Kano ta biya Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero diyyar naira Miliyan 10, sakamakon ta ke masa hakki da tsoratar da shi.

Kadaura24 ta rawaito tunda farko dai Lauyan mai kara Barr. Mamman Lawan Yusuf ya shigar da karar ne a madadin Alhaji Aminu Ado Bayero yana rokon Kotu da ta bi masa hakkinsa na Dan’adam da yake zargin an ta ke masa.

A karar da ya shigar Alhaji Aminu Ado Bayero yace umarnin da gwamnan kano ya bayar na sanyan yan sanda su kama shi, ba tare da ya aikata wani laifi ba, inda ya ce hakan ya saba da sashi na 4 na kundin tsarin mulkin Nigeria .

Bayan sauraron rokon, Kotun ta yi hukuncin cewa Gwamnantin jihar Kano ta biya mai karar Naira miliyan 10, sannan yana da damar yin yawo a ko ina a Najeria.

Daga bisani Kotun ta bayyana cewa tana da ikon Sauraran Shari’ar da Sarki na 15 ya shigar

Bayan fito wa daga Kotun Lauyan Aminu Ado, Abdurrazak Ahmad, ya shaida wa jaridar manema labarai cewar kotun ta yadda lallai gwamnatin jahar Kano, ta keta hurimin da dokar kasa ta ba wa sarki na 15, don a kama shi har sai da ingantaccen dalili.

Kazalika Lauyan Gwamnatin Jahar Kano Barr Ibrahim Isa Wangida ya bayyana cewa, wannan hukuncin da kotun ta yi nasara ce a Gare su , domin ba a taba mutuncin sarkin Kano na 16 Muhammadu Sunusi ii ba, inda ma su karar suka roki kotun ta cire shi daga gidansa amma kotun bata bayar da damar hakan ba.

Ya Kara da cewa za su sanar da wadanda suke wakilta , idan da akwai yiwuwar daukaka kara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *