July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Marayu da zaurawa sama 270 ne suka amfana da naman Sallah – Kwamared Usman Dalhatu

1 min read

Inwar tallafawa marayu Gajiyayyu da zaurawa dake Unguwa Medile ta bukaci al’umma musamman masu hannu da shuni dama sauran al’umma dasu tallafawa irin wadannan kungiyoyi domin rage irin matsanancin halin da al’umma suke fuskanta.

Shugaban kungiyar Kwamared Usman Dalhatu ne ya bayyana haka a yayin rabon naman sallah ga iyayen marayu da zaurawa karo na takwas a ofishin kungiyar a jiya.

Usman Dalhatu ya kuma ce a bana mutane dari biyu 272 ne suka amfana da tallafin naman wanda kuma kungiyar ke kara kira ga mawadata dasu kara dagewa.
Tallafin wanda al’umma suke tarawa ne a don haka akwai bukatar shigowar al’umma cikin lamarin.

Wasu daga cikin wadanda suka amfana da tallafin sun bayyana farin cikin su da wannan tallafi, inda kuma suka bukaci sauran al’umma dasu tallafa musu.

A yayin rabon tallafin an raba lambobin yabo ga wasu mutane da suke baiwa kungiyar gudunmawa a koda yaushe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *