July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ana fargabar Ɗakin wasu matasa da ɗakin Girki a wani Gida sun ƙone ƙurmus a Kano

2 min read

Wata Gobara da ta tashi ta kone ɗakin kwanan wasu matasa da kuma ɗakin girki ƙurmus, a wani gida da ke gidan Maza a karamar hukumar Birni da ke jihar Kano, tare da asarar tarin dukiyoyi.

A zantawar wakilinmu Ibrahim Abdullahi Soron Dinki da matar gidan mai suna Mariya Ishak, ta ce gobarar ta tashi ne yau sakamakon kawowar wutar lantarki, al’amarin da yasa dukkanin kayayyakin da suke cikin ɗakunan suka ƙone ƙurmus.

Ta ce kayayyakin da suka ƙone sun haɗar da kayan sawar matasan da kuma Katifu, da sauran kayayyaki, wanda a lokacin da wutar ta tashi matasan sun tafi harkokin kasuwancin su.

Sai dai matar ta ce da taimakon mazauna yankin ne aka samu nasarar kashe gobarar ba tare da ta tsallaka sauran ɓangarori ko kuma tsallakawa makotan su ba, kuma ba a samu asarar rayuka ko rauni ba.

Akan al’amarin ne wakilin Dala FM Kano Hassan Mamuda Ya’u, ya zanta da mai magana da yawun hukumar kashe Gobara ta jihar Kano, PFS Saminu Yusif Abdullahi, inda ya ce akwai bukatar al’umma su rinka kiyayewa wajen amfani da kayayyakin wuta domin kaucewa tashin Gobara a muhallan su.

Ya kuma yi kira ga al’umma da cewa, duk lokacin da aka dauke wutar lantarki su tabbata sun kashe makunnin wato Soket, kafun dawowar wutar lantarkin domin gujewa tashin Gobara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *