July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mun koyar da Matasan da aka sallama daga gidan ajiya da gyaran hali sana’o’in dogaro dakai ne domin su tsaya da kafar su – Positive pathway Initiative Rukayya Umar

2 min read

Gidauniyyar ta Positive Pathway da hadin Gwiwa da UNICEF da Kuma Ma’aikatar mata da Kananan Yara ta Jihar kano Sun horos da matasa da dama da aka sallama daga gidan ajiya da gyaran hali sana’o’in dogaro dakai.

Shugaban Gidauniyyar Hajiya Rukayya Umar Tofa ce, ta bayyana haka, a yayin taron yaye daliban da suka amfana da sana’o’in dogaro kai.

Hajiya Rukayya ta ce sun koyar da Matasan sana’ar daukar hoto da sauran abubuwan da ya shafi na’ura mai kwakwalwa wato computer.

Ta Kuma ce, an kuma koyar dasu sana’ar hada takalmi da jaka domin su dogara da kansu wanda ta hakane kawai zai magance matsalolin da matasa ke fuskanta na rashin aikin yi da zaman banza da shaye-shaye da kwacen waya.

Rukayya ta ce Gidauniyyar su a kullum burin su shi ne marasa galihu daga ko wani bangare sun samu kulawa, kamar yadda sauran al’umma ke gudanar a ko da yaushe.

Wasu daga cikin iyayen Matasan da suka amfana da wannan horo sun bayyana jindadin matuka bisa wannan aikin Alheri da Gidauniyyar positive pathway ta shiryawa yaran na su.

Suma Matasan da aka koyar dasu wannan sana’a ta dogaro dakai sun bayyana farin cikin su tare da tabbatar da cewa sun koyi sana’ar da zasu ringa gudanar a ko da yaushe.

Akwai dai bukatar masu hanu da shuni da suka dage wajen tallafawa irin wadannan matasa dama sauran marasa galihu dake cikin al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *