July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mun dakatar da ayyukan ƙungiyar da take yaɗa auren jinsi – Gwamnatin Kano

1 min read

Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da ayyukan duk wasu kungiyoyin turawa da suke fakewa da ayyukan agaji suna yaɗa Baɗala a tsakanin al’umma.

Gwamnatin Kano ta bakin babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Sheikh Aminu Ibrahahim Daurawa, a yayin wata ganawa kan matsayar Gwamnatin Kano da Kuma Hukumar Hisbah dangane da wata kungiyar turawa ta WISE, da ake zargin tana fakewa da taimakawa mata da Marayu tana yada auren jinsi a jihar Kano.

A cewar sa, “Gwamnatin Kano da hukumar Hisbah basa goyon bayan yarjejeniyar SAMOA, da Gwamnatin tarayya ta shiga tsakaninta da ƙasashen turai, “in ji shi”.

Sheik Aminu Ibrahahim Daurawa, ya kuma ce sun gano cewa makirci ne aka shiryowa jihohin arewacin Najeriya, musamman ma waɗanda suke shari’ar muslunci wanda kuma jihar Kano ce a kan gaba.

“Zamu ɗauki mataki a kan wani jami’in mu da ya taɓa zuwa taron waccan ƙungiya ta WISE, a karan kansa amma Kuma ya yi jawabi da sunan Hisbah, bayan kammala taron har ma kuma fai-fan bidiyonsa ya rinƙa zagayawa a shafikan sada zumunta, “in ji Daurawa”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *