July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

NERC za ta hukunta kamfanonin rarraba lantarki kan karancin wuta a Najeriya

1 min read

What

Hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya NERC, ta gargadi kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) da cewa za su fuskanci hukunci idan ba su yi amfani da aƙalla kashi 95 cikin 100 na makamashin da aka ware musu domin samar da wutar lantarki ga jama’a a kowanne wata ba.

Wannan wani ɓangare ne na sabon umarnin hukumar NERC kan tsarin sa ido kan ayyuka rarraba wutar lantarkin.

Hukumar ta ce duk kamfanin rarraba wutar lantarki da ya kasa cika wannan ƙofa na samar da wuta zai ga raguwar kashi 5 cikin 100 a cikin kuɗin gudanarwa da ayyukan su na kwata na gaba.

NERC ta gabatar da ma’auni bakwai masu mahimmanci (KPIs) don tantance ayyukan kamfanonin.

NERC ta jaddada cewa hukunta kamfanonin ya zama dole don kiyaye tsarin kasuwa da ɗorewar kudi.

Hukumar ta kuma ce rashin mayar da hankali da kuma martani a kan ƙorafe-ƙorafen mabuƙaci zai haifar da cin tara a kullum daga ₦1,000 zuwa 10,000.

NERC ta ƙarar da cewa rashin bin ka’ida na kuma iya haifar da korar jami’an da ke da alhaki.

Shugaban NERC, Sanusi Garba, ya sanya hannu kan wannan umarni ne a ranar 5 ga Yulin 2024, inda ya jaddada ƙudirin hukumar na tabbatar da tsauraran matakan tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *