July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Za a koma jigilar dabbobi ta jirgin ƙasa – NRC

1 min read

Hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta Najeriya ta ce zata fara jigilar dabbobi daga yankin Arewa zuwa kudancin ƙasar.

Shugaban hukumar, Fidet Okhiria ya bayyana hakan a yayin wata hira da gidan talabijin ɗin Channel da safiyar ranar Laraba.

Ya ce za a riƙa yin jigilar ne ta layin dogon Warri-Itakpe.

Hukumar ta NRC ta dakatar jigilar dabbobi ta jiragen ƙasa ne a 2017 bayan matsalolin da aka samu da layin dogon da kuma na’urori.

Okhiria, ya ce layin dogon Warri zuwa itakpe zai koma ɗaukar dabbobi nan da wata ɗaya zuwa biyu wanda zai taimakawa makiyaya safarar dabbobinsu daga yankin Arewa ta tsakiya zuwa kudanci Najeriya.

A ranar Talata shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana shirin ƙirƙirar sabuwar ma’aikata da zata bunƙasa kiwon dabobi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *