April 26, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kungiyar janbulo ta nada Bilal Nasidi Muazu a matsayin sakatare

1 min read

Kungiyar janbulo network for better tomorrow ta nada Bilal Nasidi Muazu a matsayin sabon sakataren kungiyar.

A wata Sanarwa da shugaban kungiyar Dr Ahmad Ismail ya sanyawa hannu ya ce nada Bilal Nasidi Muazu ya Samo asali ne da irin gudunmawa da yake bawa al’ummar ta janbulo.


Ya Kara da cewa Bilal Nasidi Muazu shi ne Dan Asalin unguwar Janbulo da ya wakilci Jihar Kano a musabakar Alqur’ani mai girman Wanda ya gudana a Jihar Lagos Wanda ya Kare a matsayi na uku a shekara ta 2018.


Ya kuma tallafawa Makarantun Islamiyya da dama a Unguwar wajen karantawa da kuma Makarantun matan aure guda biyu.

Dan jarida Bilal Nasidi Muazu Wanda yake aiki a tashar Freedom radio ya kawo wa kungiyar tallafi daga bangaren gwamnati Jihar Kano a shekara ta 2019.

A nasa jawabin Wakilin Bilal Nasidi Mu’azu a wajen taron Al Ameen Nasidi Muazu ya godewa Allah bisa wannan karramawa tare da tabbatar wa kungiyar cigaba da nuna kwazo a ko wani irin lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *