May 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Muna kan nazarin sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi – PDP tsagin Aminu Wali

1 min read

Jam’iyyar PDP ta jihar Kano tsagin Aminu Wali ta ce, tana tattara bayanai domin ɗaukar mataki na gaba kan sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi.

Shugaban tsagin Muhammina Baƙo Lamiɗo ne ya bayyana hakan ga Wakilin mu Al Ameen Nasidi.

Lamiɗo ya ce, dama an saba hakan, duk inda aka yi zaɓen ƙananan hukumomi jam’iyya mai mulki ta lashe baki ɗaya.

Sai dai ya ce, ya zama tilas su shiga a matsayinsu na ƴan adawa da tsammanin ko za a yi musu adalci.

A halin yanzu ya ce, suna tsaka tattara bayanai kan zaɓen domin ɗaukar matakin da ya dace.

Tsagin jam’iyyar na tsohon gwamna Kwankwaso dai sun ƙauracewa zaɓen, ta ha har ƙin shiga takara sannan suka umarci mabiya su ƙauracewa rumfunan zaɓe.

Sai dai Lamiɗo ya ce, su sun shiga kuma an yi zaɓe tare da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *