May 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gobarar da ta tashi a babbar kasuwar Sokoto ‘ta laƙume miliyoyin naira’

2 min read

Gobara ta tashi a babbar kasuwar Sokoto da ke arewacin
Najeriya, lamarin da ya janyo asarar dukiya ta miliyoyin naira.
Bayanai sun ce gobarar ta tashi ne da safiyar yau Talata kuma
zuwa lokacin wannan rahoto, wutar na ci gaba da ci.
A hukumance, ba a san musababbin tashin gobarar ba, sai dai
bayanai sun ce gobarar ta soma tashi ne daga Kofar Yan
Roba.
Jami’an hukumar kashe gobara sun gargzaya kasuwar inda
suka yi ta kokarin kashe wutar.
Naru Bello, wani dan kasuwa ne da ke da shago a kasuwar, ya
shaida wa BBC cewa gobarar ta tashi da misalin karfe bakwai
na safe kuma ta cinye dukkan kayan da ke shagonsa da ma na
wasu abokan sana’arsa.
Ya ce masu kashe gobarar sun fuskanci kalubale saboda
yadda aka gina shaguna a kan hanya.
Shi ma Zaiyanu Yahaya Assada, wanda daya ne daga cikin ‘yan
kasuwar, ya ce gobarar ta kona kusan daukacin kayansa yana
mai cewa barayi suna shiga suna sata.
Shugaban gudanarwa a babbar kasuwar ta birnin Sokoto, Alhaji
Ibrahim mil Goma, ya ce ‘yan kasuwar ne da kansu suka lalata
hanyoyin da ke ciki kasuwar shi ya sa masu aikin kashe gobara
suke shan wahala wurin kashe ta.
A cewarsa, gwamnati ta yi bakin kokarinta wajen gyara
kasuwar.
Gwamnan jihar ta Sokoto, Aminu Waziri tambuwal, wanda ya
ziyarci kasuwar, ya kuma jajanta wa ‘yan kasuwar ta Sokoto
Central Market bisa wannan ibtila’i.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *