July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

A Yau ake bai wa Najeriya shaidar rabuwa da cutar polio

3 min read

Ana sa ran a ranar Talata 25 ne wata hukuma ta musamman mai
zaman kanta ta kasa da kasa kan yaki da cutar polio wato Shan Inna
za ta yi shela a hukumance cewa Najeriya ta rabu da cutar, abin da
ke nufin yanzu babu kwayar cutar ta polio a ilahirin nahiyar Afirka.
Da ma Najeriya ce kasar da ta rage mai cutar a Afirka, amma yanzu
fiye da shekaru uku ba a samu ko da yaro daya da ya kamu da ita ba,
yayin da aka kwashe shekaru da dama ana aikin riga-kafi.
Kafin yanzu dai sai da jami’an hukumar Lafiya ta Duniya WHO suka
ziyarci Najeriya domin tantance ayyukan da kasar ta yi. Muddin aka
ba Najeriya shaidar, to a duniya baki daya zai kasance saura
kasashen Afghanistan da Pakistan masu cutar.
Da ma kasashen Najeriya da Afghanistan da Pakistan ne suka rage a
duniya masu wannan nau’in a duniya a cewar WHO, amma kusan
shekaru hudu ke nan Najeriya ba ta sake samun shi wannan nau’in
ba abinda ya kawo ta ga matakin na gab da samun shaida rabuwa da
ita. A tsakiyar wannan shekarar ne dai dama Hukumar Lafiya ta Duniya
WHO ta ce ta amince da takardun neman shaidar rabuwa da cutar
shan-Inna wato Polio da kasashen Najeriya da Kamaru da Sudan ta
Kudu da kuma Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka suka gabatar mata.
WHO ta ce takardu da kuma bayanan da kasashen na Afirka suka
gabatar sun cika dukkan sharudan ayyana su a matsayin wadanda ba
su da cutar polio, amma dai ana bukatar karin bitar yanayin da suke
ciki kafin a bayar da sanarwa ta karshe kan matsayinsu game da
cutar mai nakasa yara.
WHO ta ce wannan wani lokaci mai cikke da tarihi ga Afirka da kuma
yunkurin kawar da cutar ta Shann Inna daga doron kasa.
Sai dai kuma Hukumar bayar da shaidar rabuwa da polio ta Sashen
Afirka za ta sake duba bayanan da kasashen suka gabatar, ana kuma
sa ran hukumar bada shaidar mai zaman kanta ta zata bai wa
nahiyar Afirka shaida ta rabuwa da polio a cikin watan Agusta, bayan
an kammala tsare-tsaren masu wuyan sha’ani.
Muddin a karshe aka ayyna Afirka a matsayin wadda ta rabu da cutar
polio, haka zai kasance wata muhimmiyar gaba a yunkurin kawar daA watan Agustan 2019 ne dai Najeriya ta cika shekara uku ba tare da
samun wani mai dauke da kwayar cutar polio ba.
Wannan ranar dai tana da muhimmancin gaske kasancewar a tsarin
hukumar lafiya ta duniya (WHO), dole sai kasa ta shafe shekara uku
ba tare da kamuwa da cutar ba kafin a iya ayyana ta a matsayin
wacce ba kwayar polio a cikinta.
To sai dai dole sai WHO ta gudanar da bincike domin tabbatar da
lamarin kafin ta iya bayyana cewa ba a samu bullar cutar a cikin
shekaru uku ba a kasar.
A shekarar 2012, Najeriya na da a kalla mutum 223 da suka kamu da
polio wato rabin adadin wadanda ke da polio duk duniya kenan a
cewar WHO.
Kwararru dai sun alakanta wannan nasarar da raguwar rikice-rikice
da ake yi da mayakan kungiyar Boko Haram.
Rikicin da ake yi da kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin
Najeriya ne ya sa magunguna ba sa isa wasu yankunan jihar Borno.
Borno dai ita ce jiha wacce aka fi samun mutanen da suka kamu da
Polio. A ranar 21 ga watan Augustar shekarar 2016 ne aka samu
mutum na karshe wanda ya kamu da polio.
cutar a fadin duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *