May 3, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kafa ƙungiyar samari masu tsuke aljihu salon rowa ne – ƴan mata

2 min read

Tattaunawar Khalifa Shehu Dokaji da matasa Hafsa Aliyu da
Umar Faruk Al-ikhwani
Wani batu da a baya-bayan nan ya karaɗe shafukan sada
zumunta musamman Tuwita shi ne ɓullar wata sabuwar
ƙungiya ta maza marowata da a Turancin Ingilishi ake kira da
Stingy Men Association of Nigeria.
Wannan dai ya sa ana ta tafka muhawara a shafukan da har
aka ƙirƙiri maudu’in #stingymenasoociationofNigeria wanda ya
samu karɓuwa a shafukan Facebook da Tuwita ɗin.
Sai dai batun na ci gaba da faɗaɗa inda ko a Kano, ake tafka
mahawara tsakanin samari da ƴan mata kan ƙungiyar samari
masu matse bakin aljihu ko masu dunƙule hannu da ya zuwa
yanzu take da mabiya sama da dubu 120.
Matasan masu dunƙule hannu sun ce sun kafa ƙungiyar ne don
kawo ƙarshen yaudarar ‘yan mata, waɗanda suka mayar da su
saniyar tatsa.
Cikin wata tattaunawa ta musamman, BBC ta yi hira da wasu
matasa biyu – Hafsa Aliyu da Umar Faruk Al-ikhwani, shugaban
ƙungiyar ta samari masu matse bakin aljihu a jihar Kano inda
kowannensu ya bayyana matsayarsa.
Dalilin kafa ƙungiyar
A cewar Umar Faruk Al-ikhwani, maƙasudin ƙirƙirar ita wannan
ƙungiya na da nasaba da matsalolin da matasa suke fuskanta
da kuma yadda mata suke jibga musu ɗawainiyarsu.
Ya ce za ka ga “yarinya ta tara samari sama da biyar kuma
kowanne akwai hidimar da take buƙata ya yi mata, misali za ka
ga yarinya tana da ƙawaye da aka yi musu aure da samari
kuma kowanne ta tsara wane shi zai yi mata ankon wance”.
Ya bayyana cewa manufar ƙungiyar ita ce yaƙi da yaudara ka
ga ke nan idan aka magance buɗe bakin aljihu zai zama an
saita ƴan matan ta yadda za su tsaya da saurayi ɗaya.
Sai dai Hafsa Aliyu ta ce akwai son zuciya a yadda samarin
suka haɗu suka kafa ƙungiyar saboda a ganinta, “idan kana son
mutum da gaske, sadakin so shi ne kyauta don ka yi wa abin
da kake so kyauta wannan ba laifi bane”.
Ta ce ƙungiyar ta ɓullo da wani salo na rowa ne saboda a
tsarin rayuwa, duk wanda za ka zauna da shi “kana buƙatar ka
more shi ya more ka” wanda Al-ikhwani ya ce sam ƙungiyar ba
ta nemi matasa su yi rowa ba illa dai tana nemansu ne su saita
bakin aljihu ta yadda za su tunkari yarinyar da suke son aura da
kyakkyawar manufa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *