May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Zargin Rashawa: Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano ta ba da shawarar Cire MD ARTV

2 min read

Hukumar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta shawarci shugaban ma’aikata na jihar ya nada jami’in da zai kula da gidan talabijin Abubakar Rimi mallakin gwamnatin jihar kano, bayan cire shugaban gidan talabijin din na yanzu.

Shawarar hukumar ta biyo bayan binciken da hukumar ta ke yi akan Manajan Daraktan gidan talabijin na ARTV Mustapha Ibrahim indabawa da wasu ma’aikatan gudanarwar da aka bankado ayyukan cin hanci da rashawar da suka yi.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawan ta ba da umarnin a kulle ofishin Manajan Daraktan gidan talabijin din domin gudun dakile binciken da ake gudanarwa.

Na yi imanin kowane lokaci daga yanzu shugabanmu zai mika sakamakon binciken da shawarwari ga gwamna.” A cewar wata majiyar kadaura24

Ya bayyana cewa ‘’Binciken da ake gudanarwa ya kara nuna cewa gidan talabijin din na samar da kudaden shiga masu yawa, yayin da aka gano ma’aikata da dama da basa komai a tashar.

Wani jami’in da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa Majiyar kadaura24 cewa Manajan Daraktan, Mustapha Ibrahim Indabawa, da wasu ma’aikatan gudanarwa sun fara mayar da kudaden da haramun din da ake zargin sun dauka daga asusun gidan talabijin din.

Majiyar ta kara da cewa “A yanzu haka mun samu nasarar kwato sama da N3.5m daga hannun wasu ma’aikatan yayin da manajan daraktan ya dawo da kusan N100,000 yana mai cewa bai karkatar da kudin da ake zargin an karkatar ba, Amma kuma ya yarda ya mika motocinsa na alfarma ga hukumar ​ ko kuma ya sayar da ita ya mayar da kuɗin, ”

Majiyar ta ci gaba da cewa, Hukumar yaki da cin hanci da rashawar ta ki amincewa MD ya ajiyar motar tasa, inda yace zata aminta da abun da ya zo da shi din ba”.

Hukumar karbar korafe-korafen da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta kai ziyarar ba zata gidan talabijin din na ARTV, biyo bayan korafin da Kungiyoyin NUJ da RATTAWU suka hada gwiwa suka shigar kan wanda ya kai ga gano almundahanar kudade sama da Naira miliyan N100.

Independent Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *